IQNA

Mutane Sun Karbi Baje Kolin Adabi Rubuta Kissa Na Tunawa Da Imam Khomeini ® A Sudan

Bangaren adabi da fasaha: a daidai lokacin bayyana kaddamar da baje kolin adabi da rubuta gajeriyar kissa dangane tunawa da mu'assashin jamhuriyar Musulunci ta Iran Imam Khomeini ® a kasar Sudan fiye da yadda aka yi zato mutane da daman e suka bayyana kauna da aniyarsu ta shiga wannan kasuwar baje kolin.




Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran Ikna ne ya watsa rahoton cewa; a daidai lokacin bayyana kaddamar da baje kolin adabi da rubuta gajeriyar kissa dangane tunawa da mu'assashin jamhuriyar Musulunci ta Iran Imam Khomeini ® a kasar Sudan fiye da yadda aka yi zato mutane da daman e suka bayyana kauna da aniyarsu ta shiga wannan kasuwar baje kolin. A matakin farko mutane saba'in da daya ne suka cika sharuddan shiga wannan gasar ada shiga a gobza da su a cikin wannan gasar da mutane uku ne za su samu kyauta wato na daya da na biyu da na uku kuma a ranar ashirin da bakwai ga watan bahman na shekara ta dubu daya da dari uku da tamanin da tara hijira shamsiya ne za a fara gudanar da wannann gasar.

744184