IQNA

Taro Kan Nasarar Juyin Juya Halin Musulunci A Iran A Kasar Canada

Bangaren al'adu da fasaha, An gudanar da zaman taro kan samun nasarar juyin juya halin Musulunci a kasar Canada, tare da halartar wasu daga malaman addini da kuma mabiya addinin Musulunci da ke kasar.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalt daga shafin sadarwa na yanar gizo na cibiyar raya al'adu da ilimin Musulunci an habarta cewa, an gudanar da zaman taro kan samun nasarar juyin juya halin Musulunci a kasar Canada, tare da halartar wasu daga malaman addini da kuma mabiya addinin Musulunci da ke kasar ta Canada.

Mai kula da ayyukan ofishin jakadancin jamhuriyar Musulunci ta Iran a fadar mulkin kasar Canada Sheikh hasani, ya halarci zaman taron, ya kuma gabatar da jawabi kan irin gagarumar nasarar da al'ummar suka samu wajen kawo karshen mulkin zalunci da danniya na sarki Shah.

Ya ce nasarar wannan juyi babban lamari ne ga dukkanin musulmi, kuma hakan ya dawo wa addinin Musulunci da izzarsa da kuma daukakakrsa a idon duniya, bayana da kasashe masu girman kai suka yi kokarin ganin sun murkushe shi ta wane hali.

Gudanar da zaman taro kan samun nasarar juyin juya halin Musulunci a kasar Canada, tare da halartar wasu daga malaman addini da kuma mabiya addinin Musulunci da ke kasar, babban ci gaba ne a dangantakar kasashen biyu.

747172