IQNA

Taron Kan Binciken Juyin Juya Halin Masar A Mahangar Musulunci A Alkahira

Bangaren kasa da kasa; taron binciken juyin juya halin musuluncin kasar Masar a mahangar musulunci juyin da aka gudanar a ranar ashirin da biyar ga watan Janairin shekara ta dubu biyu da goma sha daya miladiya kuma za a fara gudanar da taron ne a yau bakwai ga watan Isfand na shekara ta dubu daya da dari uku da tamanin da tara hijira shamsiya a masallacin Balal dake birnin Alkahira na Masar.


Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran Ikna ne ya watsa rahoton cewa; taron binciken juyin juya halin musuluncin kasar Masar a mahangar musulunci juyin da aka gudanar a ranar ashirin da biyar ga watan Janairin shekara ta dubu biyu da goma sha daya miladiya kuma za a fara gudanar da taron ne a yau bakwai ga watan Isfand na shekara ta dubu daya da dari uku da tamanin da tara hijira shamsiya a masallacin Balal dake birnin Alkahira na Masar. Mahalarta wannan taro za su yi nazari da bincike dalla-dalla kan juyin juya halin musulunci na kasar Masar da kuma dangantakarsa da musulunci da kuma matsayinsa a mahangar musulunci.


752611