IQNA

Ci gaba Da Gudanar Da Taron Maulidin Ma'aikin Allah (SWA) A Indiya

Bangaren al'adu da Fasaha: a kasar Indiya ana ci gaba da gudanar da tarurrukan maulidin ma'aikin Allah tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi da kuma alayan gidansa tsarkaka da kuma na jikansa Imam Ja'afar Sadik (AS) a yankuna da biranai daban daban a fadin kasar ta Indiya a ranar alhamis biyar ga watan Isfand na shekara ta dubu daya da dari uku da tamanin da tara a masallacin Muati dake tsakiyar birnin Faid Abad na wannan kasar an gudanar da irin wannan taro.



Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa; a kasar Indiya ana ci gaba da gudanar da tarurrukan maulidin ma'aikin Allah tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi da kuma alayan gidansa tsarkaka da kuma na jikansa Imam Ja'afar Sadik (AS) a yankuna da biranai daban daban a fadin kasar ta Indiya a ranar alhamis biyar ga watan Isfand na shekara ta dubu daya da dari uku da tamanin da tara a masallacin Muati dake tsakiyar birnin Faid Abad na wannan kasar an gudanar da irin wannan taro.Wannan taron maulidin ma'aikin Allah (SWA) wakilin marigayi Said Ali Damin ya shirya kuma an samu halartar mutane masu yawan gasket da suka halarci gurin wannan bukin maulidin ma'aikin Allah tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi da alayan gidansa tsarkaka.

753304