Bangaren al'adu da fasaha; sakataren cibiyar kula da ilimi da bincike a hukumar da ke kula da yada al'adun jamhuriyar musulunci ta Iran a ketare ya bayyana cewa a wannan shekara za su yi bayani da yada abubuwa na ma'anawiya na sabuwar shekarar Iraniyawa ta Noruz shekara ta hijira shamsiya a kasashen waje.
Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran Ikna ne ya watsa rahoton cewa; sakataren cibiyar kula da ilimi da bincike a hukumar da ke kula da yada al'adun jamhuriyar musulunci ta Iran a ketare ya bayyana cewa a wannan shekara za su yi bayani da yada abubuwa na ma'anawiya na sabuwar shekarar Iraniyawa ta Noruz shekara ta hijira shamsiya a kasashen waje.Muhammad Rida Dahshiri a wata tattaunwa ce da ta hada shi da kamfanin dillancin labarai na Ikna ya bayyana hakan tare da jinjina cewa wannan shekara za su himmatu wajan yada al'adun sabuwar shekara ta hijira shamsiya.
754488