IQNA

Taron Karawa Juna Sani Na Malaman Addinin Musulunci A kasar Jordan

Bangaren fikira da ilmi, An fara gudanar da wani zaman taro na karawa juna sani na malaman addinin muslunci a jami’oi daban-daban na kasashen musulmi, wanda ake gudanar a matsayi na kasa da kasa a birnin Aman na kasar Jordan.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Al-dastur ta kasar Kordan an habarta cewa, an fara gudanar da wani zaman taro na karawa juna sani na malaman addinin muslunci a jami’oi daban-daban na kasashen musulmi, wanda ake gudanar a matsayi na kasa da kasa a birnin Aman fadar mulkin kasar.
Rahoton ya ci gaba da cewa wata cibiyar malaman jami’oi da kuma hadin gwiwa da jami’ar nazari kan harkokin musulunci ta kasar Jordan ne suka dauki nauyin shirya wannan zaman taro, wanda kuma yake samun halartar masana daga sassa daban-daban na kasar da kumakasashen ketare, musamman ma daga kasashen larabawa da na musulmi.
An fara gudanar da wani zaman taro na karawa juna sani na malaman addinin muslunci a jami’oi daban-daban na kasashen musulmi, wanda ake gudanar a matsayi na kasa da kasa a birnin Aman na kasar Jordan.
759328