IQNA

An Buga Wani Littafi Kan Juyi A Mahangar Jagoran Juyin Musulunci A Afghanistan

Bangaren kasa da kasa, an buga tare da yada wani littafi kan juyin a mahanagar jagoran juyin juya halin musulunci na Iran Ayatollah Sayyid Ali Khameini (DZ) wanda aka buga a cikin yarukan farisanci da kuma pashtu a birnin Kabul fadar mulkin kasar Afghanistan.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga bangaren yada labaransa da ke birnin kabul na kasar Afghanistan cewa, an buga tare da yada wani littafi kan juyin a mahanagar jagoran juyin juya halin musulunci na Iran Ayatollah Sayyid Ali Khameini (DZ) wanda aka buga a cikin yarukan farisanci da kuma pashtu a birnin Kabul fadar mulkin kasar Afghanista, wanda wasu daga cikin masanan kasar suka dauki nauyin rubutawa da bugawa.
Bayanin ya ci gaba da cewa wani labari da ya naklato daga shafin sadarwa na yanar gizo na bangaren yada labaransa na da ke birnin Kabul cewa, ma’aikatar kula da harkokin a’adu ta kasar Afghanistan ta sanar cewa ana fara gudanar da wani zaman taro mai taken makon al’adun Iran, wanda zai gudana tare da hadin gwiwa da ma’aikatar bunkasa harkokin al’adu ta kasar Iran da ke da ofishi a birnin.
Ma’aikatar kula da harkokin a’adu ta kasar Afghanistan ta sanar cewa ana fara gudanar da wani zaman taro mai taken makon al’adun Iran, wanda zai gudana tare da hadin gwiwa da ma’aikatar bunkasa harkokin al’adu ta kasar Iran suka dauki nauyin gudanarwa.
762806