Bangaren fikira, an buga tare da yada littafin marigayi Imam Khomeni (RA) da ke yin bayani kan fikirar addini a wannan zamani da muke ciki, haka nan kuma da fadakar da al’umma muhimman abubuwan da duniyarmu ta yau take ciki.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, an buga tare da yada littafin marigayi Imam Khomeni (RA) da ke yin bayani kan fikirar addini a wannan zamani da muke ciki, haka nan kuma da fadakar da al’umma muhimman abubuwan da duniyarmu ta yau take ciki.
A bangare guda kuma an gudanar da wani zaman taro na makon hadin kai tsakanin al’ummar musulmi a babban masallacin Hifield da ke cikin birnin harare fadar mulkin kasar Zimbabwe a mahangar marigayi Imam Khomeini (RA) daidai da lokacin gudanar da tarukan maulidin manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iayalan gidansa tsarkaka.
Bayanin ya ci gaba da cewa, zaman taron wanda aka gudanar a birnin Harare, ya samu halartar mutane da suka hada malamai da kuma sauran mabiya a ddinin musulunci mazauna kasar da kuma ‘yan asalin kasar,inda suka saurari bayanai da aka gabatara wajen taron.
An gudanar da wani zaman taro na makon hadin kai tsakanin al’ummar musulmi a babban masallacin Hifield da ke cikin birnin harare fadar mulkin kasar Zimbabwe a mahangar marigayi Imam Khomeini (RA) daidai da lokacin gudanar da tarukan maulidi.
765007