Bangaren kasa da kasa; a ranar ashirin da bakwai ga watan Farvardin na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in za a gudanar da taron binciken hanyoyin da ake amfani da su wajan harder karatun kur'ani a jami'ar fasaha ta birnin London na kasar Britaniya.
Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin kur'ani a mai girma a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ikna ta watsa rahoton cewa; a ranar ashirin da bakwai ga watan Farvardin na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in za a gudanar da taron binciken hanyoyin da ake amfani da su wajan harder karatun kur'ani a jami'ar fasaha ta birnin London na kasar Britaniya. Wannan taro za a gudanar da shi ne a wannan rana da misalign karfe tara na safe da kuma zuwa karfe shidda da rabi na yamma kuma halarta taron za su yi nazari da bincike kan hanyoyin da ake amfani da su wajan harda da kuma yadda za a inganta lamarin harda a jami'ar.
767803