Bangaren al'adu da fasaha: an gudanar da kasuwar baje koli na abubuwan tarihi na Palasdinawa a birnin Beirut fadar mulkin kasar Labanon kuma kungiyoyi da cibiyoyi masu zaman kansu ne suka shirya da gudanarwa.
Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin kur'ani a mai girma a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ikna ta watsa rahoton cewa; an gudanar da kasuwar baje koli na abubuwan tarihi na Palasdinawa a birnin Beirut fadar mulkin kasar Labanon kuma kungiyoyi da cibiyoyi masu zaman kansu ne suka shirya da gudanarwa. A wajan wannan kasuwar baje kolin an nuna abubuwa masu yawan gasket da suka shafi al'ummar Palasdinu da kuma yadda wannan al'umma ked a tsawon tarihi da kima a tarihi.
767759