Bangaren kasa da kasa: a karo na dari biyu mujallar wata wata ta harshen larabci da ta kumshi addini da al'adu ,zamantakewa da abubuwa da suka shafi iyali ta fito da wannnan karon mujallar Attahira ta yi bincike kan abubuwan da suka shafi zamantakewa da mata a musulunci da cibiyar yin nazarin musulunci da ke karkashin hukumar kula da al'adu da dangantakar musulunci ta shirya.
Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani mai girma a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa; a karo na dari biyu mujallar wata wata ta harshen larabci da ta kumshi addini da al'adu ,zamantakewa da abubuwa da suka shafi iyali ta fito da wannnan karon mujallar Attahira ta yi bincike kan abubuwan da suka shafi zamantakewa da mata a musulunci da cibiyar yin nazarin musulunci da ke karkashin hukumar kula da al'adu da dangantakar musulunci ta shirya.Wannan mujallata ta Attahira da ake bugawa da harshen larabci ta kumshi abubuwa masu yawan gasket da suka shafi al'adu ,addini,zamantakewa da kuma matsayi da rawar da mata ke takawa a musulunci da sauran lamura daban-daban .
770123