IQNA

Taron Baje Kolin Yawon Shakatawa Na Kasa Da Kasa A Georgia

Bangaren al’adu da fasaha, An fara gudanar da wani taron baje koli na yawon shakatawa a kasar Georgia wanda ake gudanarwa amataki na kasa da kasa, tare da halartar wakilan kamfanonin yawon shakatawa na kasashen musulmi musamman daga yankin gabas ta tsakiya, inda Iran ta gabatar muhimman abubuwa da suka danganci yawon shakatawa a cikin kasarta.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a rahotoon ya da ya samu ta yanar gizo an habarta cewa, an fara gudanar da wani taron baje koli na yawon shakatawa a kasar Georgia wanda ake gudanarwa amataki na kasa da kasa, tare da halartar wakilan kamfanonin yawon shakatawa na kasashen musulmi musamman daga yankin gabas ta tsakiya, inda Iran ta gabatar muhimman abubuwa da suka danganci yawon shakatawa a cikin kasarta da suke da dangata da tarihi.
Bayanin ya ci gaba da cewa wannan zaman taro zai yi dubi kan hanyoyin da ya kamata a bi domin saka hannayen jari wanda hakan zai iya habbaka dukkanin bangarori na yawon shakatawa da bude a cikin kasashen musulmi, musamman idan aka yi la’akari da irin muhimmancin da wannan bangare yake da shi a cikin kasashen musulmi.
Za a gudanar da wani taron kara juna sani a karon farkon kan saka hannayen jari a bangaren yawon shakatawa a kasashen musulmi, wanda ake sa ran zai gudana a birnin Demascus fadar mulkin kasar Syria tare da halartar masana da kuma ‘yan kasuwa masu saka hannayen jari na kasashen ketare.
774467