IQNA

Za A Gina Masallaci Zai Ci Masallata Dubu Uku A Kasar Faransa

Bangaren kasa da kasa, za a gina masallaci da zai dauki masallata dubu uku a kasar Faransa wanda babbar cibiyar kula da ayyukan muslunci ta kasar za ta dauki nauyin gudanarwa a birnin Charlevelle na kasar, da nufin kara karfafa gwiwar musulmin yankin wajen kula da harkokin addininsu.


Kamfanin dillanicn labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na musulmin kasar Fransa an bayyana cewa, za a gina masallaci da zai dauki masallata dubu uku a kasar Faransa wanda babbar cibiyar kula da ayyukan muslunci ta kasar za ta dauki nauyin gudanarwa a birnin Charlevelle na kasar, da nufin kara karfafa gwiwar musulmin yankin wajen kula da harkokin addininsu, bisa laa'akari da irin kalubalen da suke fuskanta.

Bayanin ya ci gaba da cewa dukkanin mabiya addinin muslunci na kasar Faransa suna kokawa dangane da irin banbancin da aka fara nuna musu tun bayan da shugaban kasar mai ci yanzu Nikola Saerky ya karbi ragamar shugabancin kasar, inda suke kallonsa a matsayin wani mai matukar nuna banbanci da wariya ga mabiya addinin Musulunci.

Za a gina masallaci da zai dauki masallata dubu uku a kasar Faransa wanda babbar cibiyar kula da ayyukan muslunci ta kasar za ta dauki nauyin gudanarwa a birnin Charlevelle na kasar, da nufin kara karfafa gwiwar musulmin yankin wajen kula da harkokin addininsu a kasar.

776464