Bangaren al'adu da fasaha: Umra Lukman ministan da ke kula da harkokin musulmi a Filipine a lokacin wata ganawa da ya yi da Huseini Divsalar mai kula da ofishin yada al'adun Iran a wannan kasa ya bayyana cewa: aiki tare da tuntubar juna a tsakanin mabiya addinai daban-daban a duniya ko shakka babu zai taimaka wajan tabbatar da sulhu da kwanciyar hankali a duniya.
Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: Umra Lukman ministan da ke kula da harkokin musulmi a Filipine a lokacin wata ganawa da ya yi da Huseini Divsalar mai kula da ofishin yada al'adun Iran a wannan kasa ya bayyana cewa: aiki tare da tuntubar juna a tsakanin mabiya addinai daban-daban a duniya ko shakka babu zai taimaka wajan tabbatar da sulhu da kwanciyar hankali a duniya.Daya daga cikin rikice-rikicen da duniya take fuskanta ta fuskar zamantakewa da kuma sauran bangarori na rayuwa sun samo asali ne daga rashin fahimtar juna da kusanci a tsakanin mabiya addinai daban daban a duniya kuma matukar aka karfafa wannan fanno za a samu bakin zaren magance duk wani riukici da samar da sulhu da kwanciyar hankali a duniya.
776386