Bangaren siyasa da zamantakewa;Aygun Suleymanova Malamar makaranta a yankin Hovsan da ke garin Baku fadar mulkin kasar Jamhuriyar Azarbeijan an kore tad a dakatar da ita daga koyarwa a wannan makaranta saboda tan a sanye da hijabi da kuma yadda ta nuna za ta ci gaba da yin riko da farillar sanya hijabin musulunci.
Kamfanin dillacin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa; Aygun Suleymanova Malamar makaranta a yankin Hovsan da ke garin Baku fadar mulkin kasar Jamhuriyar Azarbeijan an kore tad a dakatar da ita daga koyarwa a wannan makaranta saboda tan a sanye da hijabi da kuma yadda ta nuna za ta ci gaba da yin riko da farillar sanya hijabin musulunci. Shugaban makarantar ne ya dauki wannan mataki na nuna wariya da banbanci kan wannan baiwar Allah musulma ba tare da ta yi wani laifi a wajan koyarwa da bawa yara tarbiya ko kin yin biyayya ga tsarin koyarwa da tsarin makaranta kawai laifinta tana sanye da hijabin musulunci kuma a ranar lotinin sha biyu ga watan urdebehesht na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya ne shuagaban makarantar ya kafa mata sharadin cewa: idan tana son ci gaba da koyarwa a makarantar dole ta daina sanya hijabin musulunci ko kuma an kore ta. Irin wannna mataki na fito wa a fili da nuni yadda ake nunawa musulmi da addinin musulunci karan tsana da halin wariya a duniya.
786372