Bangaren kasa da kasa:an wallafa da watsa littafin makarantun likitanci a cikin wayewar musulunci da bangaren watsa da wallafa littafai na hukumar koyarwa da yada al'adun musulunci Asesko ta watsa.
Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa; an wallafa da watsa littafin makarantun likitanci a cikin wayewar musulunci da bangaren watsa da wallafa littafai na hukumar koyarwa da yada al'adun musulunci Asesko ta watsa.
Wannan littafi day a kumshi shafuka dari biyu da hamsin da takwas day a hada makaloli da aka gabatar a taron hukumar ta Asesko a birnin Trablus a shekara ta dubu biyu da shidda miladiya.Har ila yau ya kumshi bayanai da jawabai daban da ban da suka shafi binciki da nazari.
787689