Bangaren kasa da kasa: A kasar faransa an wallafa da kuma watsa littafin da ke Magana da yaren kurmanci na nuni da kuma yake bayani kan addinin musulunci.
Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran Ikna ne ya watsa rahoton cewa; A kasar faransa an wallafa da kuma watsa littafin da ke Magana da yaren kurmanci na nuni da kuma yake bayani kan addinin musulunci.wannan littafi mai suna donne moi un signe ya kumshi shafuka dari da biyar kuma yana koyar da yadda za a yi Magana da yaren nuni yaren kurmanci da kuma ya yi bayani dalla-dalla kan addinin musulunci da kuma yadda za a fadakar da wadanda ba su iya Magana da kuma yadda za su fahimci addini.
788432