Bangaren kasa da kasa:A karo na sha bakwai a kasar Masar a ranar sha takwas ga watan Urdebehesht na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in shekara ta hijira shamsiya aka fara gudanar da taro kan muijizar kur'ani mai tsarki kan fannonin ilimi da kuma hadisan ma'aikin Allah tsira da aminicin Allah ya tabbata a gare shi da kuma alayansa kuma a jami'ar kuduncin Alwadi a garin Kana na Masar ake gudanar da wannan taro.
Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran Ikna ne ya watsa rahoton cewa; A karo na sha bakwai a kasar Masar a ranar sha takwas ga watan Urdebehesht na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in shekara ta hijira shamsiya aka fara gudanar da taro kan muijizar kur'ani mai tsarki kan fannonin ilimi da kuma hadisan ma'aikin Allah tsira da aminicin Allah ya tabbata a gare shi da kuma alayansa kuma a jami'ar kuduncin Alwadi a garin Kana na Masar ake gudanar da wannan taro.An jiwo jaridar Alyaum Sabi'I da ake bugawa a kasar ta maser ta bayyana cewa wannan taro zai kwashe kwanaki bakwai da kuma ya samu halartar kungiyoyi masu nazari kan wannan fanni inda za su yi masanyar nazari da tunani.
788729