IQNA

Faisal AlMaulawi masani Kuma Fitaccen Marubuci Dan Kasar Labanon Ya Rasu

Bangaren kasa :Faisal Almaulawi tsohon babban sakataren kungiyar al'ummar musulmin kasar Labanon kuma daya daga cikin fitattun masana da masu yada addini dan kasar Labanon bayan shekaru saba'in a duniya ya yi bankwana da wannan duniya bayan day a yi kwananinsa masu albarka.


Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran Ikna ne ya watsa rahoton cewa; Faisal Almaulawi tsohon babban sakataren kungiyar al'ummar musulmin kasar Labanon kuma daya daga cikin fitattun masana da masu yada addini dan kasar Labanon bayan shekaru saba'in a duniya ya yi bankwana da wannan duniya bayan day a yi kwananinsa masu albarka.A jiya ne aka gudanar da taron naja'izar wannan bawon Allah a babban masalallcin Almansuri da ke garin Trablus na kasar Labanon inda manyan marubuta dam asana suka halarci gurin jana'izarsa.

788904