Bangaren kasa da kasa;kotun koli a kasar Bangladesh ta yi watsi da dokar hana fitar da fatawa da malamai ke yi .
Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa; kotun koli a kasar Bangladesh ta yi watsi da dokar hana fitar da fatawa da malamai ke yi . A shekara ta dubu biyu da daya ne kotun kolin kasar ta fitar da wani hukumci na hana fitar da duk wata fatawa da malaman addinin kasar ke yi a wani mataki day a kawo kace nace da kalubalai daga malaman addinin kasar da ke ganin wani mataki ne na danniya a ke nuna masu.
790797