Bangaren kasa da kasa: babban sakataren kungiyar hadin kan kasashen musulmi a ranar biyar ga watan Khurdad na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in ya fitar da wani bayani ga manaema labarai inda ya nun adamuwa da karuwar cin zarafin da ake nunawa masu adawa da shugaban kasar Yaman Ali Abdallah Salih.
Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa; : babban sakataren kungiyar hadin kan kasashen musulmi a ranar biyar ga watan Khurdad na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in ya fitar da wani bayani ga manaema labarai inda ya nun adamuwa da karuwar cin zarafin da ake nunawa masu adawa da shugaban kasar Yaman Ali Abdallah Salih.Ikmalul Dine Ihsan Uglo babban sakataren kungioyar hadin kan kasashen musulmin ya nuna takaicinsa a fili da karuwar tashin hankali da cin zarafin da ke nuna wa masu adawa da shugaban kasar Yaman Ali Abdallah Salih da kuma yadda lamarin kasar ya kasa ci ya kasa cinyewa musamman idan aka yi la'akarin da yadda shuagab da ke fuskantar adawa daga al'ummar kasar ya ki yada dan mangwaro ya huta da guda da yawo da hankalin jama'a a ciki da wajen kasar.
799046