Bangaren siyasa da zamantakewa; wata tawaga da ta kumshi masu fitar da fatawa a kasar Albaniya da suka ziyarci jamhuriyar Kosovo a karon farko sun yi masanyar ra'ayi da masu fitar da fatawa a wannan kasar inda suka nuna kwarewa da surfin ilimi ta fuskar harkokin addini da musulunci.
Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani mai girma a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa; wata tawaga da ta kumshi masu fitar da fatawa a kasar Albaniya da suka ziyarci jamhuriyar Kosovo a karon farko sun yi masanyar ra'ayi da masu fitar da fatawa a wannan kasar inda suka nuna kwarewa da surfin ilimi ta fuskar harkokin addini da musulunci. Wannan ziyara da masu fitar da fatawa suka kai kasar Kosovo daga kasar ta albaniya zai taimaka matuka gaya wajan kara kusanci a tsakanin malamai da musulmin kasashen biyu da kuma ci gaban addnini da musulmin kasashen biyu.
801145