IQNA

Musulmin Kasar Australia Na Kokarin Ganin An Raya Tattaunawa Tsakanin Addinai

Bangaren kasa da kasa, mabiya addinin muslunci an kasar Australia, na kokarin ganin an raya tattaunawa tsakanin mabiya addinai, musamman ma ttsaknain mabiya addinan muslunci da kuma kiristanci, bisa la’akari da kusancin da ake akwai na akida tsakanin addinan biyu, wadanda suka yi imanin da Allah.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalato daga shafin sadarwa na ayanar gizo an bayyana cewa, mabiya addinin muslunci an kasar Australia, na kokarin ganin an raya tattaunawa tsakanin mabiya addinai, musamman ma ttsaknain mabiya addinan muslunci da kuma kiristanci, bisa la’akari da kusancin da ake akwai na akida tsakanin addinan biyu, wadanda suka yi imanin da Allah madaukakin sarki.
A bangare guda kuma a wani rahoto da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na meoc an bayyana cewa, ana shirin fara gudanar da wani zaman taro kan kara wa juna sani kan ilmomin kur'ani mai tsarki a babban dakin taruka na jami'ar Cambrirge da ke birnin London na kasar Birtaniya, wanda zai samu halartar masana daga sassa daban-daban na kasar ta Birtaniya da ma wasu kasashen ketare.
Mabiya addidinin Musulunci na kasar Birtaniya na iyakacin kokarinsu domin safke nauyi da ya rataya kansu na nuna wa sauran al'ummar kasar koyarwar addinin muslunci kan lamurrra da suka danganenci rayuwa da shafi zamantakewa, lamarin da ya yi gagarumin tasirin musamman a tsakanin masana.
802706