Bangaren kasa da kasa: taron kawo sauyi da canje-canje a harkokin kudi a kasar Malaishiya da za a gudanar a ranekun bakwai da takwas ga watan Tir na wannan shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya da aka bawa wannan taron taken addini da kasuwanci kuma a birnin Kawalalampur fadar mulkin kasar ne za a gudanar da taron.
Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa; taron kawo sauyi da canje-canje a harkokin kudi a kasar Malaishiya da za a gudanar a ranekun bakwai da takwas ga watan Tir na wannan shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya da aka bawa wannan taron taken addini da kasuwanci kuma a birnin Kawalalampur fadar mulkin kasar ne za a gudanar da taron. A wajan wannan taro masana harkokin kasuwanci da kuma masana tattalin arziki za su yi nazari da binciken hanyoyin kawo sauye-sauye a harkokin tattalin arziki da kuma kasuwanci a wannan kasa.
803288