IQNA

Bankin Yada Musulunci Ya Bawa Jami'ar Azhar Kyautar Dala Dubu 300 Don yada Larabci

Bangaren kasa da kasa; bankin yada addinin musulunci a duniya karkashin wata yarjejeniya day a kulla da shugabannin jami'ar Azhar da ke birnin Alkahira na kasar Masar ya bada taimakon dalar Amerika dubu dari uku domin yada harshen larabci a matsayinsa na yaren Kur'ani mai girma.



Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa; bankin yada addinin musulunci a duniya karkashin wata yarjejeniya day a kulla da shugabannin jami'ar Azhar da ke birnin Alkahira na kasar Masar ya bada taimakon dalar Amerika dubu dari uku domin yada harshen larabci a matsayinsa na yaren Kur'ani mai girma.Daga cikin wadanda suka sa hannu kan wannan yarjejeniyar akwai Ahmad Khatib sheikhul Azzahar da kuma Ahmad Ali shugaban bankin yada addininin muslunci day a ce wannan wata manufa ce ta yada harshen larabci da kuma addinin muslunci a duniya.

809494