IQNA

Imam Ali (AS) Tun Karnonin Farko Ya Himmatu Wajan Kare Hakkoki Da Adalci

Bangaren al'adu da fasaha; Muhammad Rida Gazalisfali mai kula da oifishin yada al'adun jamhuriyar musulunci ta Iran a Seraleyon a taron da aka bawa taken Imam (AS) hasken adalaci da hakkokin bil adama ya bayyana cewa; Imam Ali (AS) tun karnonin da suka gabata ya yi fice da haskaka wannan bangare na kare hakkokin bil adam da kuma adalci a tsakanin al'umma a daidaiku da kuma a rayuwa ta jama'a.



Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin kur'ani mai girma a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa; Muhammad Rida Gazalisfali mai kula da oifishin yada al'adun jamhuriyar musulunci ta Iran a Seraleyon a taron da aka bawa taken Imam (AS) hasken adalaci da hakkokin bil adama ya bayyana cewa; Imam Ali (AS) tun karnonin da suka gabata ya yi fice da haskaka wannan bangare na kare hakkokin bil adam da kuma adalci a tsakanin al'umma a daidaiku da kuma a rayuwa ta jama'a. Wannan taro an gudanar da shi ne a ranar ashirin da biyar ga watan khurdad shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya inda ya kara da cewa ma'aikin allah tsirta da amincin Allah ya tabbata a gare shi da kuma alayan gidansa shi ne abin koyi da dukan mahaluki wajan kare hakkin mutum yayin da shi kuma imam Ali (AS) ya share karnoni yana bayani kan ma'anar adalci da kare hakkin dan adam da jaddada muhimmancin hakan.


810517