IQNA

Musulmin Tataristan Sun Raya Ranar Shigar Musulunci A Kasar

Bangaren siyasa da zamantakewa; shekaru dubu daya da dari biyu da ashirin da biyu da suka gabata ne addinin musulunci ya shiga jamhuriyar Tataristan ta hanyar garin Bolgar inda a ranar asabar din da ta gabata ashirin da takwas ga watan Khurdad shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya a gidan ajiyar kayan tarihi na gwamnati aka gudanar da taron bukin tuni da wannan rana mai muhimmanci ga al'ummar kasar.


Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa; shekaru dubu daya da dari biyu da ashirin da biyu da suka gabata ne addinin musulunci ya shiga jamhuriyar Tataristan ta hanyar garin Bolgar inda a ranar asabar din da ta gabata ashirin da takwas ga watan Khurdad shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya a gidan ajiyar kayan tarihi na gwamnati aka gudanar da taron bukin tuni da wannan rana mai muhimmanci ga al'ummar kasar. A wajan wannan buki na tuni da zagayowar ranar tarihi da kuma rana mai muhimmanci a kasar an samu halartar manyan jami'an gwamnati da kuma manyan yan siyasa da wakilan jama'a da kuma malaman addinin musulunci da suka gabatar da wajabai masu gamsarwa dangane da shigar musulunci a jamhuriyar Tataristan da kuma irin alfanon day a biyo bayan shigar addinin musulunci a kasar.

811242