Bangaren siyasa da zamantakewa; kokari na wayar da kai da fadakar da musulmi wani nauyi ne da ya rataya a wuyan masu yada addini da kuma masu tabligi na addini musamman a daidai wannan lokaci da musulmi da kungiyoyin musulmi suka ringumi gwagwarmaya da kuma fito na fito da ma'abuta girman kai masu mulkin danniya.
Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: kokari na wayar da kai da fadakar da musulmi wani nauyi ne da ya rataya a wuyan masu yada addini da kuma masu tabligi na addini musamman a daidai wannan lokaci da musulmi da kungiyoyin musulmi suka ringumi gwagwarmaya da kuma fito na fito da ma'abuta girman kai masu mulkin danniya.A yau an kara samin wayewa da kuma fadakarwa daga kungiyoyi da musulmi a duniya musulmi musamman a kasashen larabawa kama daga arewacin Afrika ya zuwa yankin gabas ta tsakiya don haka wata babbar dama da lokaci ne mai kyau ga masu yada addini da kuma tabligi na su tashi domin fadakar da jama'a don tashi daga barci.
816227