IQNA

Hukumar Kula Da Hulda A Tsakanin Musulmi Ta Yi Allah Wadai Da Mamaye Masallacin Kudus

Bangaren kasa da kasa:hukumar da ke kula da dangantaka da kuma hulda a tsakanin musulmi a ranar ashirin da takawas ga watan Shahrivar na shekarar hijira shamsiya ta dubu daya da dari uku da tis'in ta fitar da wani bayani da a cikinsa take yin Allah wadai da harin mamaye da wasu yahudawan sahyoniya yan share guri zauna suka kai wa masallacin kudus mai tsarki.




Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin kur'ani mai girma a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: hukumar da ke kula da dangantaka da kuma hulda a tsakanin musulmi a ranar ashirin da takawas ga watan Shahrivar na shekarar hijira shamsiya ta dubu daya da dari uku da tis'in ta fitar da wani bayani da a cikinsa take yin Allah wadai da harin mamaye da wasu yahudawan sahyoniya yan share guri zauna suka kai wa masallacin kudus mai tsarki. Sakataren kungiyar hadin kan kasashen musulmi ne da kansa Ikmaluldine Ihsan Uglo ya fitar da baynin cewa; yahudawan Sahyoniya ne yan share guri zauna suka kai wa Masallacin harin a wani matakin neman tada fitina da takalar fada da kuma cin fuska da mutuncin musulmi ne a duniya da kuma ya saba dokokin kasa da kasa na mutunta gurare masu tsarki na addini.


864227