Bangaren kasa da kasa; Sheikh Nabil Kavuk mataimakin komitin zartarwa da ayyuka a kungiyar hizbullahi a kasar Labanon ya bayyana cewa wannan ziyarar aiki da Bashara Batris Alra'I shugaban kirsitoci mabiya tarikar Maroni a kasar Labanon ya kai a yankin kuduncin Labanon ta shiga tarihi kuma wata hanaya ce ta karfafa dangantaka da yan uwantaka a tsakanin al'ummar Labanon.
Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa; Sheikh Nabil Kavuk mataimakin komitin zartarwa da ayyuka a kungiyar hizbullahi a kasar Labanon ya bayyana cewa wannan ziyarar aiki da Bashara Batris Alra'I shugaban kirsitoci mabiya tarikar Maroni a kasar Labanon ya kai a yankin kuduncin Labanon ta shiga tarihi kuma wata hanaya ce ta karfafa dangantaka da yan uwantaka a tsakanin al'ummar Labanon. Ya kara da cewa wannan ziyara ce da ta bakantawa gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila da rai domin ta jima tana fadi tashin ganin ba a samu hadin kai da fahimtar juna tsakanin yan kasar Labanon musamman musulmi da kiristoci amman wannan ziyara ta nuni fatar al'ummar Labanon na hada kai da dangantaka da junansu don tabbatar da zaman lafiya.
867388