Bangaren kasa da kasa: taron gaggauwa na ministocin ilimi mai zurfi na kasashen musulmi za a gudanar da shi a ranekun sha biyu da sha uku ga watan Maher na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya a birnin Riyad fadar mulkin kasar Saudiya.
Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ikna ne ya watsa rahoton cewa: taron gaggauwa na ministocin ilimi mai zurfi na kasashen musulmi za a gudanar da shi a ranekun sha biyu da sha uku ga watan Maher na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya a birnin Riyad fadar mulkin kasar Saudiya.Kamar yadda aka nakalto daga shafin Internet na ISESCO wannan taron gaggauwa za a samu halartar hukumar tuntubar juna ta kungiyar hadin kan kasashen musulmi,reshen koyarwa da yada ilimi da al'adu na Asesco da kuma ma'aikatun ilimi mai zurfi ta kasashen musulmi da kuma ta Saudiya. Daga cikin abubuwa da za a tattauna a gurin wannan taro sun hada da yin nazarin hanyoyin da za a inganta sha'anin ilimi musamman na jami'o'I a kasashen musulmi tare da fito da wani tsari na bai daya.
870358