Bangaren kasa da kasa: wasu daga cikin kungiyoyi a kasar Bahrain da kuma na kasa da kasa sun shirya wani taro a birnin Beirut na kasar Labanon da a lokacin gudanar da wannan taro za su yi nazari da bincike kan ta'addancin da gwamnatin Ali Khalifa ta tabka da kuma hanyayin gurfanar da wadanda suka aikata wannan aika-aika karkashin dokoki.
Kamfanin dillancin labarai na ikna ne dake kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ya watsa rahoton cewa: wasu daga cikin kungiyoyi a kasar Bahrain da kuma na kasa da kasa sun shirya wani taro a birnin Beirut na kasar Labanon da a lokacin gudanar da wannan taro za su yi nazari da bincike kan ta'addancin da gwamnatin Ali Khalifa ta tabka da kuma hanyayin gurfanar da wadanda suka aikata wannan aika-aika karkashin dokoki.A ranekun sha uku da sha hudu ga watan Mehr na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya za su gudanar da wannan taro inda manyan baki a ciki da wajan kasar ta labanon za su halarci wannan taro da kuma shugabannin kungiyoyin fararen hula da na kare hakkokin bil adam.
872202