IQNA

Baje Kolin Kasa Da Kasa Ta Abincin Halal A Faransa

Bangaren kasa kasa: a karo na tara za a gudanar da kasuwar baje kolin abinci na halaliya a ranekun sha biyar da sha shidda ga watan Farvardin na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in da daya a birnin Paris fadar mulkin kasar Faransa.



Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani mai tsarki a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa; a karo na tara za a gudanar da kasuwar baje kolin abinci na halaliya a ranekun sha biyar da sha shidda ga watan Farvardin na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in da daya a birnin Paris fadar mulkin kasar Faransa. Kamfanin Paris Halal Expro ne ya dauki nauyi na gudanar da wannan kasuwar baje koli karo na tara na kasa da aksa da zai hada kimanin kamfanoni saba'in da suka shafi yin abubuwan cid a sha na halaliya da kuma aka kula da tsabta da kiwon lafiya da kuma uwa uba suka kiyaye dokoki addinin musulunci kuma za su fit one daga kasashen nahiyar Turai domin halartar wannan taro.

875539