IQNA

Baje Kolin Littafai Na Musulunci Karo Na Hudu A Indiya

Bangaren kasa da kasa: a karo na hudu ana gudanar da kasuwar baje koli ta littafan musulunci a birnin Dehlu Fadar mulkin kasar Indiya inda cibiyar yada al'adun musulunci da watsa littafai ta Husna ta shirya.



Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani mai tsarki a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa; a karo na hudu ana gudanar da kasuwar baje koli ta littafan musulunci a birnin Dehlu Fadar mulkin kasar Indiya inda cibiyar yada al'adun musulunci da watsa littafai ta Husna ta shirya.A wajan wannan kasuwar baje kolin an kawo littafai masu yawa kuma da suka shafi addinin musulunci da kuma suka hada da littafan da suke Magana da bayani kan kissoshin kur'ani domin yara kanana da kuma wani bangare na kissoshin Kur'ani domin nucuwar zukatan yara kanana da dai sauran littafai makamantan haka.

875406