IQNA

Taron Tattaunawar Al'adu A Garjistan

Bangaren al'adu da fasaha; taron kasa da kasa kan tattaunawar al'adu da aka buda a ranar ashirin da shidda ga watan Meher na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira a dakin taro na jami'ar gwmanti ta Yakub Gugubashawili da ke lardin Kakhati Garjistan aka farad a za a kwashe kwanaki uku ana gudanar da taron.


Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: taron kasa da kasa kan tattaunawar al'adu da aka buda a ranar ashirin da shidda ga watan Meher na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira a dakin taro na jami'ar gwmanti ta Yakub Gugubashawili da ke lardin Kakhati Garjistan aka farad a za a kwashe kwanaki uku ana gudanar da taron.Wannan taro ne da zai yi nazari da binciken hanyoyin binkasa hanyar tattaunawa da fahimtar juna a tsakanin al'ummomin duniya musamman musulmi da kuma habaka hanyar tattaunawa da kusanci a tsakanin kabilu daban daban .Kuma wajan wannan taro an samu halartar masana ilimi da yan jami'a da wakilan kungiyoyi da jam'iyu.

882936