IQNA

Kyautar Samar Da Sulhu Ta Calabi An Bawa KhaKham Na Albaniya

Bangaren siyasa da zamantakewa; kyautar samara da sulhu da zamanlafiya ta Calabi a wannan karo a shekara ta dubu biyu da sha daya miladiya wato shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya an bawa Khakham waltar Humulaka shugaban jami'ar Abraham Gaygar a kasar Jamus.
Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa; kyautar samara da sulhu da zamanlafiya ta Calabi a wannan karo a shekara ta dubu biyu da sha daya miladiya wato shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya an bawa Khakham waltar Humulaka shugaban jami'ar Abraham Gaygar a kasar Jamus.A ranar daya ga watan Aban na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya ne shugaban na jami'ar Abraham gaygar ya karbi wannan kyautar da aka jijina masa kan jan aikin da yake gudanarwa a hanyar tabbatar da sulhu .Kuma ya samu wannan kyautar ne karkashin sakamakon da alkalai guda uku mabiya addinai mabanbanta suka fitar inda suka yi amanna da cewa shi ne ya cancanci karbar wannan kyautar a wannan karo.Har ila yau wannan kyautar ana bayar da ita ne shekaru uku ga wanda ya taka rawar gani ta fuskar samara da zaman lafiya a duniya.


885907