IQNA

Wata Tawagar malam Labanon Sun Isa Vatikan

Bangaren kasa da kasa; wata tawaga da ta kumshi malaman shi'a da sunna daga kasar Labanon ta isa fadar Vatikan da ke kasar Italiya domin halartar wani taron kasa da kasa na tattaunawar addinai da aka fara a jiya biyu ga watan Aban na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya.

Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa; wata tawaga da ta kumshi malaman shi'a da sunna daga kasar Labanon ta isa fadar Vatikan da ke kasar Italiya domin halartar wani taron kasa da kasa na tattaunawar addinai da aka fara a jiya biyu ga watan Aban na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya.Wannan tawaga ta hada da Sheikh Ahmad Kablan babban malamin tarikar Ja'afariya da Muhammad Samak mai bawa mai fitar da fatawa Abas Halbi shawarta kuma alkali masanin harkokin kare hakkin dan adam suna daga cikin wadanda suka halarci wannan taron tattaunawa na kasa da kasa tsakanin mabiya addinai a duniya karo na ashirin da biyar.

886652