Bangaren kasa da kasa: hukumomi a kasar Saudiya a jiya ne tara ga watan Aban na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya ta saki Usam Al'atar dan shi'a mazaunin kasar Kanada kuma sun kama shi ne saboda ya soki akidar wahabiyawa a madina.
Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran Ikna ne ya watsa rahoton cewa: hukumomi a kasar Saudiya a jiya ne tara ga watan Aban na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya ta saki Usam Al'atar dan shi'a mazaunin kasar Kanada kuma sun kama shi ne saboda ya soki akidar wahabiyawa a madina. A ranar takawas ga watan Aban ne a birnin Madina a gaban sauran takwarorinsa mahajjata ya gabatar da jawabi da a cikinsa yake sukar siyasar gwamnatin Saudiya da kuma akidar wahabiyanci masu wuce gona da iri kuma an sake shi ne a jiya bayan da ofishin jakadancin Kanada a birnin Riyad na Saudiya ya sa baki .
891103