IQNA

Zaman Nazari Kan Bunkasa Harkokin Tarjamar Littafan Addini A Iran

Bangaren al'adu, an gudanar da wani zama a kasar Iran dangane da bunkasa harkokin tarjamar littafan addinin muslunci da aka rubuta a cikin harsunan laraci da farisanci zuwa wasu harsunan na daban.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, an gudanar da wani zama a kasar Iran dangane da bunkasa harkokin tarjamar littafan addinin muslunci da aka rubuta a cikin harsunan laraci da farisanci zuwa wasu harsunan na daban da nufin yada al'adu da koyarwar muslunci a tsakanin al'ummomin duniya.
A can kasar Bahrain kuma, Al'ummar kasar na ci gaba da gudanar da zanga-zangar lumana domin neman sauyi na demokradiyya a kasar, duk kuwa da irin matakan da mahukuntan kasar suke dauka domin murkushe yunkurin nasu.

Rahotanni daga kasar ta Bahrain sun tabbatar da cewa a jiya dubban mutane sun fito a yankuna daban-daban na kasar Bahrain a kan tituna suna kira ga mahukuntan kasar da su gaggauta sakin fursunonin siyasar da suke tsare da su, musamman kananan yara mata da suka kame a cikin wannan mako, bisa zargin cewa suna da dangataka da masu neman sauyi.

Mutanen kasar Bahrain da kuma wasu kungiyoyin kare hakkin bil adama na kasashen larabawa, suna ci gaba da yin Allawadai da halin ko-in-kula da kungiyar hadin kan kasashen larabawa take nunawa, kan kisan kiyashin da mahukuntan Bahrain tare da taimakon Saudiyya suke yi kan fararen hular kasar masu neman sauyi ta hanyar lumana.

898827