IQNA

Kare Ma Talatakawa hakkokinsu Na Siyasa Shi Kan Gaba

Bangaren kasa da kasa: limamin juma'a a kasar baharain a ranar juma'a ashirin da bakwai ga watan aban na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in a sallar juma'a ya jaddada cewa: hakkokin siyasa na daga cikin hakkoki na sahun gaba da al'ummar kasar ke bukatar a kiyaye masu da kuma suke bukatar gwamnati da ta kiyaye kuma babu wani hakkin da zai iya maye wannan kuma maido da wasu hakkoki da aka kwace a baya ba sai sa a yafe wannan hakkin ba.





Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: limamin juma'a a kasar baharain a ranar juma'a ashirin da bakwai ga watan aban na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in a sallar juma'a ya jaddada cewa: hakkokin siyasa na daga cikin hakkoki na sahun gaba da al'ummar kasar ke bukatar a kiyaye masu da kuma suke bukatar gwamnati da ta kiyaye kuma babu wani hakkin da zai iya maye wannan kuma maido da wasu hakkoki da aka kwace a baya ba sai sa a yafe wannan hakkin ba.Ayatullahu Isa Kasim limamin juma'a a kasar Bahrain ya kara da cewa; wasu abubuwa na hakika da kuma na gaskiya ana canja akalarsu da karyayyaki a daidai lokacin da kowa ya san ba haka ne kuma kowa yana gani yadda al'ummar kasar ta baharin ke fitowa kan tituna domin bayyana abubuwan da suke so da bukatar kawo canji a lamarin siyasar kasar da kuma yadda gwamnatin Ali Khalifa ke kisan gilla da zubar da jinin fafaren hula.

900427