Bangaren kasa da kasa; yadda said hasan Nasarullahi babban sakataren kungiyar gwagwarmaya ta Hizbullahi a kasar Labanon ya sadaukar da dansa kan hanayr Allah ya tabbatar da kara fito da fuskar gwagwarmaya da kara karfafa ta a fili kuma ya kara tabbatar da cewa shi da iyalansa a kullum a shirye suke su kare karamar al'umma da kasar Labanon da addini.
Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa; yadda said hasan Nasarullahi babban sakataren kungiyar gwagwarmaya ta Hizbullahi a kasar Labanon ya sadaukar da dansa kan hanayr Allah ya tabbatar da kara fito da fuskar gwagwarmaya da kara karfafa ta a fili kuma ya kara tabbatar da cewa shi da iyalansa a kullum a shirye suke su kare karamar al'umma da kasar Labanon da addini.Hujjatullahi wal muslim Ali Rida Bi Niyaz wakilin jami'ar Almustapha (SWA) al'alamiya a kasar Suriya kuma shugaban hauzar ilimi ta Imam Khomeini ® awannan kasar a wata tattaunawa day a yi da kamfanin labarai na Ikna ne ya yi wannan bayani da kara bayyana cewa wannan shi ne ya bayyana kyakkyawar manufa da niyar babban sakataren kungiyra da kuma kokarinsa na kare mutunci da karamar kasar Labanon da addini kan duk wani wuce gonad a irin makiya.
907554