IQNA

An Jaddada Wajibcin Kare Hadin Kai A Pakistan A Lokacin Muharram

Bangaren kasa da kasa;a ranar juma'a sha daya ga watan Azar shekara ta dubu daya dari uku da tis'in hijira shamsiya a wani zama da masu shiryawa da halartar taro kan muharram a garin Rawulpandi na kasar Pakistan sun jaddada wajibcin kare hadin kai a tsakanin al'ummomin musulmi a wannan lokaci na ranekun Muharram.



Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa; a ranar juma'a sha daya ga watan Azar shekara ta dubu daya dari uku da tis'in hijira shamsiya a wani zama da masu shiryawa da halartar taro kan muharram a garin Rawulpandi na kasar Pakistan sun jaddada wajibcin kare hadin kai a tsakanin al'ummomin musulmi a wannan lokaci na ranekun Muharram.har ila yau sun kara jaddada cewa a wadannan raneku na Muharram ya dace musulmi a ko ina suke da su nunawa junansu yan uwantaka da hadin kai da kuma kyautatawa juna a tsakaninsu ,Kuma wannan taro an gudanar da shi ne tsakanin yan shi'a da suna yan kasar inda manyan malamai da masana suka halarta tare da gabatar da bayanai masu gamsarwa .


909635