Bangaren siyasa da zamantakewa: ofishin da ke kula da yada al'adun jamhuriyar musulunci ta Iran a Beirut fadar mulkin kasar Labanon ya bayyana cewa; akwai darussa masu yawa da za a dauka a ranar Ashura daya daga cikin irin wadannan darussa akwai rashin hankali da rundunar zalunci ta nuna kan Imam Huseini (AS) da iyalan gidansa da kuma sahabbansa da duk wani mai hankali da tunani da basira zai tausaya da daukan darasi.
Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa; ofishin da ke kula da yada al'adun jamhuriyar musulunci ta Iran a Beirut fadar mulkin kasar Labanon ya bayyana cewa; akwai darussa masu yawa da za a dauka a ranar Ashura daya daga cikin irin wadannan darussa akwai rashin hankali da rundunar zalunci ta nuna kan Imam Huseini (AS) da iyalan gidansa da kuma sahabbansa da duk wani mai hankali da tunani da basira zai tausaya da daukan darasi.A wani taron na musamman ne dangane da ranar ashura Hujjatul Islam da musulmi Husein Ra'is zade mai kula da ofishin yada al'adun jamhuriyar musulunci ta Iran a birnin na Beirut ya bayyana cewa; darusa a ranar ashura suna da yawa kama daka bangaren akida yada addini,manufa da cimma buri da fadakar da jama'a da kuma ilimantarwa ta bangarori daban daban.
909738