Bangaren al’adu da fasaha, an buga wani littafi na musamman wanda yake yin magana kan waki’ar Ashura da kuma abubuwan da suka wakana a lokacin wannan waki’a mai girma.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na banagren bunkasa harkokin al’adu na karamin ofishin jakadancin Iran da ke birnin Baku na kasar azarbaijan cewa, an buga wani littafi na musamman wanda yake yin magana kan waki’ar Ashura da kuma abubuwan da suka wakana a lokacin wannan waki’a mai girma da ta shafi dukkanin muslumin duniya baki daya.
Wannan littafi mai dauke da bayanai kan muhimmancin sanin ranar Ashura da kuma dukkanin abubuwan da suka afku a wannn rana, an buga shi ne a cikin shafuka goma sha shida, kuma an yi shi a cikin kwafi dubu daya 1000, da nufin rarra su ga dukkanin musulmi da suke bukata, daga bisani kuma ana sa ransake buga wani adadi mai yawa.
Buga wani littafi na musamman wanda yake yin magana kan waki’ar Ashura da kuma abubuwan da suka wakana a lokacin wannan waki’a mai girma, na da matukar muhimamnci ga musulmin wannan kasa, da suke da bukatar sanin hakinin abin d ake nufi da Ashura, domin kuwa kasarinsu mabiya tafarkin iyalan gidan amnzon allah ne.
910600