Bangaren kasa da kasa; kungiyoyi da jam'iyoyin siyasa a kasar Bahrain sun fitar da wata sanarwa ta bai daya ta yin Allah wadai da yadda sojojin haya na Ali Khalifa suka kai wa masu gudanar da taron juyayin Husaini (AS) a Huseiniya a kasar hari.
Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa; kungiyoyi da jam'iyoyin siyasa a kasar Bahrain sun fitar da wata sanarwa ta bai daya ta yin Allah wadai da yadda sojojin haya na Ali Khalifa suka kai wa masu gudanar da taron juyayin Husaini (AS) a Huseiniya a kasar hari.A cikin wannan sanarwa sun nuna takaicinsu a fili da yadda mahukumtan kasar da kuma gwamnatin kasar Bahrain ke daukan matakan rashin sani da kuma nuna rashin tausayi kan fararen hula da kuma kisan gilla kansu musamman a daidai wannan lokaci na juyayin zalunci na karshe da aka nuna Imam Huseini (AS) da kuma iyalan gidansa da sahabbansa a yankin karbala.
910671