IQNA

An Rufe Masallacin Muhammadiya A kasar Tajikistan

Bangaren siyasa da zamantakewa; a ci gaba da siyasar nuna adawa da wariya kan yan shi'a da gwamnatin Tajikistan ke yi ta rufe babban masallacin Muhammadiya karkashin zargin gudanar da ayyukan da tarurrukan ashura ta juyayin kisan gillar da aka yi wa Imam Huseini (AS) kuma gwamnatin kasar ce ta sanar da daukan wannan mataki na rufe masallaci har zuwa watanni uku a nan gaba.





Kamfanin dillancin labarai na ikana da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: a ci gaba da siyasar nuna adawa da wariya kan yan shi'a da gwamnatin Tajikistan ke yi ta rufe babban masallacin Muhammadiya karkashin zargin gudanar da ayyukan da tarurrukan ashura ta juyayin kisan gillar da aka yi wa Imam Huseini (AS) kuma gwamnatin kasar ce ta sanar da daukan wannan mataki na rufe masallaci har zuwa watanni uku a nan gaba.A ranar ashirin ga watan azar na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya ne mahukumatan kasar ta Tajikistan suka dauki wannan mataki.Haji Akbar Ture Janzade tsohon mai fitar da fatawa a wannan kasa kuma daya daga cikin malamai fitattu a yankin a ranar ashirin daya ga watan azar a wata tattaunawa da kamfanin dillancin labarai na Ikana ya bayyana cewa: a baya bayan nan komitin a gwamnati ta kafa mai kula da harkokin addini ya aike da wata wasika ta jan kunne kan gudanar da tarurrukan addini na Ashura a wannan masallaci na Muhammadiya kuma karkashin dokokin jamhuriyar Tajikistan da suka shafi yanci akida da ayyukan hukumomi da cibiyoyin addini ta dakatar da wannan masallaci na tsawon watanni uku.


914800