IQNA

Fadada Tsarin Kudi Na Musulunci A Kasashen Gabacin Afrika

Bangaren siyasa da zamantakewa: a ci gaba da kokarin fadada tsarin banki da hulda ta saye da sayarwa da kuma ajiyar kudade bayan bude bankin musulunci na Amana a kasar Tanzaniya ana ci gaba da kokarin fadada wannan shiri na bankin musulunci a tsakanin kasashen yankin gabacin Afrika .



Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa; a ci gaba da kokarin fadada tsarin banki da hulda ta saye da sayarwa da kuma ajiyar kudade bayan bude bankin musulunci na Amana a kasar Tanzaniya ana ci gaba da kokarin fadada wannan shiri na bankin musulunci a tsakanin kasashen yankin gabacin Afrika .Asad Ahmad shugaban bankin musulunci ta kasar Keniya Gulf African Bank a ranar ashirin da daya ga watan aban na wannan shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya a cikin wani taron manema labarai day a gabatar ya bayyana cewa: suna kokarin ganin sun fadada wannan shiri da tsari na kafa bankin musulunci a tsakanin kasashen yankin gabacin Afrika. Don kafa sun bayan da suka bude sabbin reshen bankin a kasashen Keniya da Tanzaniya a halin yanzu kuma za su bude irin wannan reshe a kasar Uganda kamar yadda za su ci gaba da wannan shiri a sauran kasashen yankin.


917151