IQNA

Likitoci Musulmi A Garuruwan Indiya Na Yi Wa Jama'a Magani Kyauta

Bangaren siyasa da zamantakewa: a ranar talatin ga watan azar na wannan shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya a daidai ranar zagayowar shahadar imam Zainul abidina (AS) likitoci da masu jiyar maras lafiya musulmi za su yi wa al'ummomin yankin Bandra a garin Banbai a lardin Maharashta na kasar indiya magani kyauta.



Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula d aharkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: a ranar talatin ga watan azar na wannan shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya a daidai ranar zagayowar shahadar imam Zainul abidina (AS) likitoci da masu jiyar maras lafiya musulmi za su yi wa al'ummomin yankin Bandra a garin Banbai a lardin Maharashta na kasar indiya magani kyauta:al'ummar yankin za a yi masu magani kyauta a Abu Mohammad Foundation da kuma dakin yin jiya na Kaneez Fatima Hospital da kuma tuni mutanan yankin suka nuna jin dadinsu kan wannan mataki da wannan kokari na yabo da taimakawa jama'a da ganinsa a wani kokari da abin yabo da cewa ya kamata sauran gurare da cibiyoyin sham magani da jiya su yi koyi da irin wannan mataki da wadannan cibiyoyi suka dauka na tallafawa jama'ar yankin.

916581