IQNA

Gwamnatin Maroko Ta Haramta Expres Ta Faransa Da Ta Ci Mutuncin Ma'aikin Allah (SWA)

Bangaren kasa da kasa;gwamnatin Marokko ta hana sayar a sayi duk wani abu day a fito daga Express ta faransa saboda cin fusta da mutuncin ma'aikin Allah tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi da alayan gidansa a wani mataki na nuna fushin al'ummar kasar kan wannan aiki na takalar fada kan musulmin duniya.




Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin kur'ani mai girma a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: gwamnatin Marokko ta hana sayar a sayi duk wani abu day a fito daga Express ta faransa saboda cin fusta da mutuncin ma'aikin Allah tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi da alayan gidansa a wani mataki na nuna fushin al'ummar kasar kan wannan aiki na takalar fada kan musulmin duniya.Khalid Nasiri ministan sadarwa kuma kakakin gwamnatin Marokko a ranar uku ga watan Dai na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya ya bayyana cewa; shugabannin kasar ta marokko sun haramta saye da sayar da jaridar Express ta kasar Faransa saboda sharhin da suka yi kan hoton cin mutunci da aka yi wa ma'aikin Allah tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi da alayan gidansa tsarkaka kuma wata jaridar kasar Faransa ce ta sanya wannan hotuna na cin fuska ga ma'aikin Allah a wata fitowa ta musamman domin rarrabawa a cikin kasashen larabawa domin takalar fada da tayar da tashin hankali da rura wutar rikicin addini.


921896