IQNA

Taron Karawa Juna Sani Ilimi Da Makarantun Musulunci A Mali

Bangaren al'adu da fasaha:taron karawa juna sani da kokarin fadada makarantun addini tare da hadin kan kungiyar hadin kan musulunci da kula da ilimi da al'adu ta Asesko kuma daga biyar zuwa takwas ga watan Dai na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya ne za a gudanar a birnin Bamako fadar mulkin kasar Mali da ke yammacin Afrika.


Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin kur'ani mai girma a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: taron karawa juna sani da kokarin fadada makarantun addini tare da hadin kan kungiyar hadin kan musulunci da kula da ilimi da al'adu ta Asesko kuma daga biyar zuwa takwas ga watan Dai na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya ne za a gudanar a birnin Bamako fadar mulkin kasar Mali da ke yammacin Afrika.Wannan taro ya hada shugabannin makarantun addinin musulunci daga kasashen Aljeriya,Tunusiya,Senegal,Guine,Guine Bisau ,Burkina Faso, Marokko ,Mauritaniya da kuma mai masabkin baki kasar Mali.Burin gudanar da wannan taron karawa juna sani shi ne bayyana rawar da malamai ke takawa da kuma matsayin makarantun addini a ci gaban al'umma da kuma binciken hanyoyin fadada wannan fanni da magance irin matsalolin da suke fuskanta a kasashensu.

922024